fbpx
Tuesday, March 28
Shadow

Ba zamu bari mutane su mallaki Bindiga ba saboda matsalar tsaro zata karu>>Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin tarayya tace ba zata bari mutane su mallaki bindiga ba saboda hakan zai kara yawan matsalar tsaron da ake fama da itane maimakon ta ragu.

 

Ministan harkokin ‘yansanda, Muhammad Dingyadi ne ya bayyana haka.

 

Ya bayyana hakane a zama da ‘yan Majalisar wakilai, wanda shugaban masu rinjaye na majalisar, Alhassan Ado Doguwa ya jagoranta.

 

Doguwa yayi kiran a bar mutane su rike Bindiga dan kare kansu.

 

Saidai Dinyadi Yace a yanzu suna ma kokarin ganin kananan makaman dake hannun mutane sun ragu ne, kamata yayi kawai a bar jami’an tsaro su rika ta’ammuli da makamai.

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *