fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

Ba zamu bi Gwamna Umahi zuwa APC ba>>’Yan Majalisar Jihar Ebonyi

‘Yan Majalisar Jihar Ebonyi sun bayyana cewa ba zasu bi gwamnan jihar,  Dave Umahi zuwa Jam’iyyar APC ba.

 

Sun bayyana hakane a sanarwar da suka fitar jiya a Abuja wajan taro na musamman da suka yi. Shugaban ‘yan majalisar da suka fito daga jihar, Sanata Sam Egwu ya bayyana cewa, da sanatoci da ‘yan majalisar wakilai na jihar ba zasu koma jam’iyyar APC ba.

 

Yace tabbas suna da ra’ayin cewa kowace jam’iyya a 2023 ta tsayar da dan takarar shugaban kasa daga yankinsu amma wannan ba dalili bane da zai sa su juyawa jam’iyyar su baya ba.

Karanta wannan  Kiristoci Sun Taya Musulman Gyaran Fili A Kudancin Kaduna A Shirye-shiryen Sallar Idi

Yace gwamnan shine kusan ya fi kowa morat jam’iyyar ta PDP da kuma bai kamata ya juya mata baya ba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.