fbpx
Friday, February 26
Shadow

Ba zamu dawo Arewa ba, Fulani makiyaya dake kudu suka mayarwa da dattawan Arewa martani

Biyo bayan korar da gwamnatin jihar Ondo tawa fulani daga dazukan ta da kuma harin da Sunday Igboho ya kaddamar akansu, kungiyar dattawan Arewa, NEF ta nemi Fulanin da su dawo Arewa.

 

Kungiyar har ta nemi gwamnonin Arewa su shirya karbar Fulani masu bin doka da oda. Saidai a martanin Fulanin dake zaune a kudu sun bayyana cewa basu samu wannan umarni na dattawan Arewa ba.

 

A jihar Imo, Salaiman Ibrahim wanda hadimin gwamnan jihar ne ya bayyana cewa basu samu umarnin dattawan Arewn ba sannan kuma koda sun samu basu da niyyar barin jihar.

 

Shima Shugaban kungiyar Miyetti Allah yankin kudu maso Gabas, Alhaji Gidado Siddiki ya bayyana cewa Fulani Makiyaya na zaune lafiya da jama’ar yankin.

 

Yace babu wanda ya gaya musu cewa su koma Arewa kuma basa tunanin hakan. Yace abinda kawaizai sa su koma Arewa shine idan suka ga cewa ba zasu samu tsaro a yankin da suke ba.

 

“The challenges our people are having in Southern Nigeria prompted the call or suggestion by the Northern Elders Forum. However, nobody has informed me officially. Nobody is planning to go back to the North unless we are forced to go. The only thing that will make them to go is if they feel unprotected. If there is protection, why should they go? But if there is no protection they will have no other option than to go.”

 

Hakanan a jihohin Kogi , Delta, da Ekiti ma duk shuwagabannin Fulanij sun shaida cewa ba zasu koma Arewa ba, kamar yanda Sunnews ta bayyana.

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *