fbpx
Thursday, August 11
Shadow

Ba zamu iya cire sunayen matattu daga rijistar zabe ba>>INEC

Hukumar Zabe me zaman kanta, INEC ta bayyana cewa, ba zata iya cire sunayen wanda suka mutu daga rijistarta ba.

 

Tace dalili kuwa babu kundin bayanai na mutanen da suka mutu da za’a iya dogara dashi dan cire sunayen.

 

Hakan na nufin zaben shekarar 2023 ka iya zuwa da tangarda. Saboda rijistar bata da tabbas, sannan hakan zai saka a kashe kudaden da suka wuce kima waja  shirya zaben.

 

Shugaban bangaren ilimantar da masu zabe, Festus Okoye ya nemi hadin kan ‘yan Najeriya wajan bayar da bayanan wadanda suka mutu ta yanda hakan zai taimaka a tsaftace rijistar zaben, kamar yanda Punchng ta ruwaito.

Leave a Reply

Your email address will not be published.