Kungiyar ‘yan kasuwar mai ta IPMAN ta Najeriya ta bayyana cewa memboninta ba zasu iya cigaba da sayar da litar man fetur a farashin 165 ba.
Kuma a kwanakin bayan dama membobin kungiyar na kudu maso yamma sun bayyana cewa ba zasu iya cigaba da sayar da man a farashin da gwamnatin ta yanke masu ba.
Inda shugaban kungiyar na jihar Legas, Akin Akinrinade ya tabbatar da hakan ranar litinin cewa ba zasu sayar da litar mai a kasa da naira 180 ba.
Kuma ya kara da cewa ba yanjin aiki ne yasa suka kulle gidajen mai ba yanayin kasuwar ne, kuma duk wanda yasan abinda yake a harkar mai to ba zai sayar a kasa da naira 180 ba.