Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party, Peter Obi ya mayarwa da dan takarar shugaban kasa na APC martani kan zolayarsu daya yi.
Tinubu a yakin neman zaben daya je jihar Osun ya bayyana cewa kar su zabi Labour Party domin a hakan zasu mutu a jam’iyyar tasu ta kwadago.
Yayin da shima Peter Obi ya mayar da martani cewa yaji wasu na cewa zasu mutu suna kwadago.
Shi dai kira dayake yiwa al’ummar jihar dama Najeriya bakidaya shine kar sake su sake barin wani biri yayi mulki a Najeriya.