Friday, May 29
Shadow

Ba zamu taba bari a yi taron addini da shagulgulan sallah a Kano, Legas, Ogun da Abuja ba>>Hukumar ‘yansanda

Shugaban hukumar ‘yansandan Najeriya, IGP Muhammad Adamu ya taya ‘yan Najeriya murnar kammala azumin watan Ramadana lafiya inda yace lokacine da mutane da kansu suke komawa ga Allah tare da tsakake kai.

 

Ya jajantawa mutane kan halin da Sallah ta samu mutane a ciki na cutar Coronavirus/COVID-19 inda yace kada a manta da dokokin da aka tanada.

Sanarwar hakan ta fitone daga gurin me magana da yawun hukumar,FCP Frank Nba inda ya jaddada cewa akwai dokar hana zirga-zirga da kuma hana taron addini dana al’ada da aka saba yi dan hana yaduwar cutar Coronavirus/COVID-19.

 

Yace zasu kai jami’an su guraren da ya kamata dan ganin cewa ba’a take doka ba sannan kuma zasu tsaurara tsaro a lokacin sallar da bayanya.

 

Ya kara da cewa zasu tsaurara tsaro a garuruwan Abuja, Kano, Ogun da Legas dama sauran jihohi.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *