Kasar Gambia wadda yawanci Musulmai ne suka fi yawa a cikinta, ta jaddada matsayar ta ta cewa ba zata amince da Luwadi da Madigo ba.
Hakan na zuwane bayan wasu rade-radin dake yawo kwanannan cewa kasar na shirin sassauta hukuncin da akewa masu luwadi da Madigo dan neman tallafi daga kasashen Yamma.
Ebrima Sankare wanda shine me magana da yawun gwamnatin kasar ya bayyana cewa ba gaskiya banr labaran dake cewa suna shirin amincewa da Luwadi kasar dan neman tallafin kasashen yammaba, ya bayyana kalaman da cewa na siyasane kawai dan samun karbuwa a wajan mutane, kamar yanda kamfanin dillancin labaran AFP ya ruwaito.
Yace ko sake duba dokar ba zasu yi ballantama su canja ta saboda Luwadi ya sabawa al’adun mutanen kasar.