fbpx
Thursday, July 7
Shadow

Ba zamu taba yadda ba, Kotu zamu kaika muddin ka fito takarar shugaban kasa>>Wani Inyamuri ga Goodluck Jonathan

Wani babban lauya kuma Inyamuri, Dr. Law Mefor dakw jagorantar wata kungiyar Inyamurai dake fafutuka kan shugabanci yace idan tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya fito takarar shugaban kasa a 2023 zasu kaishi kotu.

 

Ya bayyana cewa doka bata baiwa Jonathan damar zama shugaban kasa ba a nan gaba, saboda ya kammala wa’adin mulkinsa.

 

Goodluck Jonathan dai ana ta rade-radin cewa, zai shiga jam’iyyar APC inda acanne ake sa ran zai fito takarar shugaban kasa na 2023.

 

A baya dai mun ji yanda Jonathan din ke samun goyon bayan wasu manyan Gwamnoni biyu na Arewa sannan kuma wata kungiyar matasa ta yi tattaki har gidansa dake Abuja inda aka nemi ya fito takarar shugaban kasa.

Karanta wannan  Hotuna: Yanda aka yi Jana'izar Sakataren OPEC, Muhammad Barkindo

 

Hakanan akwai wanda suka ce zasu shirya tattakin mutane Miliyan 1 dan ganin sun jawo hankalin Jonathan ya fito takarar shugabancin Najeriya.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.