fbpx
Tuesday, August 9
Shadow

Da Dumi Duminsa: Matasan Arewa sun yiwa Tinubu alkawarin cewa ba zasu yi bacci ba har sai sun tabbar da cewa ya lashe zaben shekarar 2023

Kungiyar matasan Arewan ta jinjinawa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmad Tinubu kan zabar Kashim Shettima daya yi a matsayin abokin takararsa.

A ranar lahdin data gabata ne Tinubu ya zabi tsohon gwamnan jihar Bornon a matsayin abokin takarar nasa na zabe mai zuwa.

Wanda hakan yasa kiristoci suke ta cece kuce kan zabar Musulmi da Musulmi da APC tayi, kuma hakan yasa wasu ma har suka sauya sheka.

Amma matasan Arewa sun jinjina masa sun ce ba zasu bacci ba sai sun tabbatar da cewa yayi nasarar lashe zabe mai zuwa na shekarar 2023.

Leave a Reply

Your email address will not be published.