Friday, May 29
Shadow

Ba zamu yi hawan Sallah ba>>Masarautar Zazzau

Masarautar Zazzau ta bayyana cewa ba zata yi hawan Sallah a lokacin Sallah Karama ba.

 

Ta bayyana cewa hakan dalilin dokokin zaman gida da Nesa-nesa da junane da gwamnatocin Tarayya da jihohi suka saka.

Mataimakin sakataren masarautar, Dan Isan Zazzau, Alhaji Umaru Shehu Idris ne ya bayyana haka ga manema labarai.

 

Yace masarautar na jawo hankalin jama’a da su zama masu bin doka da Oda saboda wannan matakai ana daukarsu ne dan kariyar jama’a sannan Addinin mu ya koya mana Rungumar kaddara me kyau da marar kyau.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *