fbpx
Friday, August 12
Shadow

Ba zamu zabi APC ba saboda ta tsayar da ‘yan takara duka musulmai>>Kiristocin Arewa

Kiristocin Arewa sun bayyana cewa, ba zasu zabi dan takarar shugaban kasa na APC ba saboda da jam’iyyar ta tsayar da ‘yan takara duka musulmai.

 

APC ta tsayar da Bola Ahmad Tinubu wanda shi kuma ya zabo Kashim Shettima a matsayin abokin takararsa.

 

Kungiyar tace APC ta dauki wannan mataki ne dan kawai ta mayar da Kiristoci musamman na Arewa saniyar ware.

 

Sakataren kungiyar dake da membobi a jihohi 19 na Najariya,  Engr Babachir Lawal ne ya bayyana haka, yace kada Kiristocin Arewa dama na Najariya gaba daya su amincewa yaudarar APC ta son musuluntar da Najariya.

Leave a Reply

Your email address will not be published.