Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari yayi jawabi a Libson dake kasar Portugal ga ‘yan Najeriya a daren jiya.
Inda yace gwamnatinsa zata tabbatar da cewa an gudanar da zaben shekarar 2023 cikin limana ba tare da magudi ba sannan za’a bar kowa ya zabi zabinsa.
Inda shugaban kasar ya kara da cewa ba zasuyi yiwa hukumar zabe ta INEC katsalandan ba a aikin nasu zasu bari su gudanar da aikin yadda ya kamata.
Hadimin shugaba Buhari ne ya bayyana hakan, watau Garba Shehu.