fbpx
Friday, December 2
Shadow

Ba zan halarci jana’izar mahaifina mara amfani ba – Jaruma Chioma Toplis

Fitacciyar jarumar fina-finan Nollywood, Chioma Toplis, a ranar Litinin din da ta gabata ta girgiza da yawa daga cikin masoyanta da mabiyanta a lokacin da ta bayyana cewa ba za ta taba halartar jana’izar mahaifinta ba idan ya rasu.

Chioma mai zafin rai ta bayyana mahaifinta a matsayin malalaci, wawa kuma mayaudari.

Ta yi wannan bayanin ne a lokacin da take mayar da martani ga wani sakon Twitter da wani @jayritse ya wallafa.

Mutumin ya yi zargin cewa mahaifinsa dattijo ne a coci kuma mai dukan mahaifiyarsa a gida.

Da take mayar da martani a shafinsa na Twitter a shafinta na Instagram, jarumar ta ce; “Na dauka mu kadai ne ke da uba marar amfani. Shi ma Dattijo ne a coci kuma mai dukan mahaifiyarmu.

Muna cikin jirgi daya, mahaifiyata ma ta bar mahaifina saboda dalilai da yawa da suka hada da rashin mutunci, rainin hankali, zamba, wauta, da kuma duka.

Ta Kuma ce, ba zan taba halartar jana’izarsa ba, abunda ya dace da shi kawai a gina rami a binne sa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *