Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPC, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana cewa, ba zai janyewa Atiku ko Tinubu takarar shugaban kasa ba.
Yace dalili kuwa shine yana da yakinin shine zai yi nasara.
Wasu dai na kiraye-kirayen cewa ya kamata Kwankwaso ya janyewa musamman Atiku daga takarar saboda suna tunanin ba zai kai labari ba.
A wasu rahotanni ma an samu cewa, Atikun na shirin ganin yayi dukkan mai yiyuwa dan hada kai da Kwankwaso.