fbpx
Tuesday, August 9
Shadow

Ba zan koma NNPP ba – Tanko Al-Makura

Sanata Tanko Al-Makura ya yi watsi da sanarwar da aka yi a kafafen sada zumunta na yanar gizo a matsayin ‘labaran karya’ inda ake zarginsa da sauya sheka daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC) zuwa jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP).

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwar manema labarai da sakataren yada labaransa, Danjuma Joseph ya raba a ranar Litinin din da ta gabata, yana mai cewa: ‘Sanarwar da aka yi a kafafen sada zumunta na yanar gizo na sauya sheka zuwa jam’iyyar NNPP a matsayin wani labari na karya na bata sunan Tanko Al-Makura.

Karanta wannan  Dan uwan Buhari daya yi barazanar rusa APC ya fice daga jam'iyyar

Ya kuma shawarci jama’a da su yi watsi da rahoton, yana mai cewa ba shi da nufin wargaza jam’iyyar APC.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.