A jiya ne kotun daukaka kara dake jihar Osun ta bayyana cewa Adeleke ne dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP na zaben fidda gwani da suka gabatar.
Wanda bayan shari’ar jam’iyyar PDP ta jinjinwa kotun sosai bisa wannan adalcin data yi.
Inda shima dan takarar nata daya lashe zaben gwamnan jihar da aka gudanar ranar asabar ya mika godiyarsa ga daukacin al’ummar jihar.
Ademola Adeleke ya bayyana cewa ba zai taba cin amarsu ba kan yar da suka bashi har yayi nasarar doke gwamnan jihar na APC, wato Oyetola.
Kuma a jiya hukumar zabe ta bashi takaddun shaidar lashe zabe.