fbpx
Monday, August 15
Shadow

Ba zan taba hutawa ba har sai na yaye maku kuncin dake damunku, cewar shugaba Buhari

Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ba zai taba hutawa ba har sai ya tabbatar da cewa Najeriya ta fita daga kuncin da take ciki yanzu.

Ya bayyana hakan ne a sakon daya fito ta hannun hadiminsa Garba Shehu na taya Musulmi murnar zagayowar babbar Sallah.

Inda yace yana jinjinawa jami’an tsaron kasar nan mata da maza bisa kokarin da suke yi na shawo kan matsalar tsaro.

Sannan yace yana taya Musulmai murnar zagayowar babbar Sallah kuma yayi kira su roki Allah ya magance mana matsalar tsaro.

Leave a Reply

Your email address will not be published.