fbpx
Thursday, July 7
Shadow

Ba zan taba tilasawa wani daga yan wasan mu cewa sai sun maye mana gurbin Eden Hazard ba>>Lampard

Manajan Chelsea, Frank Lampard ya bayyana cewa baya danganta Ziyech da Hazard yayin daya bukaci tauraron dan wasan nashi Hakim ya cigaba da kamar yadda yake yi, kuma jajircewar dan wasan ce tasa ake sa ran zai iya mayewa Chelsea gurbin Hazard.

Chelsea tasha gwagwarmaya wurin maye gurbin Eden Hazard tunda ya koma kungiyar Real Madrid, amma yanzu har ta kai ga ana danganta Ziyech da Hazard sakamakon nasarar daya yi na cin kwallaye biyu da kuma taimakawa wurin cin kwallaye uku a wasanni biyar.

Amma duk da haka shi dai Lampard ya bayyana cewa ba zai danganta Ziyech da Hazard ba inda yake cewa “Abu mai matukar wuya a samu dan wasan da zai iya maye gurbin Hazard saboda shi din na daban ne”.

Karanta wannan  Shalelen PSG, Mbappe ya samu sabani da Messi kan sayar da Neymar a wannan kakar

“Kuma ni ba zan tana lisatawa wani daga cikin sababbin yan wasan da muka siyo ba cewa dole sai sun maye mana gurbin Eden Hazard, suma su cigaba da kokari kamar yadda suke yi”.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.