fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

Ba zata yiyu Bafulatani ya kara mulkarmu ba bayan Buhari>>’Yan Kudancin Najeriya

Kungiyar ‘yan kudanci da tsakiyar Najeriya da ake kisa da SAMBA a takaice ta bayyana cewa, ba zata yiyu bafulatani ya mulki Najeriya tsawon shekaru 8 ba kuma a sake samun wani Bafulatanin ya zama shugaban kasa ba.

 

Kungiyar tace bata yadda jam’iyyar PDP  ta baiwa bafulatani tikitin takararta na shugaban kasa ba a shekarar 2023.

 

Ga dukkan alamu dai wanan kungiya na maganane akan Atiku Abubakar.

 

Hakan ya fito ne daga bakin kakakin kungiyar, Rwang Pam Jnr inda ya bayyana cewa, zasu zargi shugabab jam’iyyar na PDP, Iyorchia Ayu idan aka tsaida bafulatani takarar shugaban kasa a 2023 kuma aka ci gaba da kashesu.

Karanta wannan  Babu dan arewar da zai zabi Peter Obi, cewar Kwankwaso

 

Sun kuma caccaki Atiku Abubakar, da Bukola Saraki, da Aminu Waziri Tambuwal, da Sanata Bala Muhammad saboda kin amincewa da maganar tsarin karba-karba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.