Shugaban kwamitin kula da sojoji na majalisar tarayya, Sanata Ali Ndume ya bayyana cewa, ba’a kai harin garin Limankara na karamar hukumar Gwoza ba.
A baya dai an samu Rahotannin dake cewa an kai harin garin har an sace ‘yansanda.
Saidai a martanin Ali Ndume yace babu ma ‘yansanda a garin, Sojoji ne kawai ke kula da garin.
Yace kuma yana samun bayanai kan yadda suke gudanar da ayyukansu dan haka maganar sace ‘yansandan ba gaskiya bane.