fbpx
Tuesday, August 9
Shadow

Ba’a taba gwamnatin dakewa ‘yan Najeriya abinda ta ga dama ba irin ta Buhari>>TUC

Kungiyar Kwadago ta TUC ta bayyana cewa a tarihin Najeriya ba’a taba gwamnatin data ke wa ‘yan Najeriya irin cin kashin data ga dama ba kamar ta Shugaba Buhari.

 

Tace kuma itace gwamnatin da ‘yan kasa suka baiwa goyon baya sosai a baya amma sai ta rika taka mutane yanda take so, da ka yi magana a turo maka jami’an tsaro su kamaka ko kuma a ci ka tarar Miliyan 5.

Hakan ya fitone daga bakin shugaban kungiyar, Quadri Olaleye da kuma sakatarenta, Musa Lawal Ozigi. Hutudole ya fahimci kungiyar tace ko kwanaki 2 da suka gabata ne ‘yan Najeriya suka gama kukan karin kudin wuta amma sai gashi kuma an kara na man Fetur.

Karanta wannan  An zargi gwamnatin Zulum da biyan malaman makaranta Albashin Naira Dubu 6

 

Tace gwamnatin kwata-kwata bata jin koken talaka. Dan haka tace tana kira ga gwamnatin data janye wannan karin farashi sannan kuma ta gayyaci membobinta dan su tattauna akan batun.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.