fbpx
Thursday, May 26
Shadow

Ba’a taba yin hazikin dan kwallo a Duniya ba kamarni”>>Cristiano Ronaldo

Dan wasan Real Madrid Cristiano Ronaldo ya ce shi ne “fitaccen dan kwallo a tarihi”, bayan da ya lashe gasar gwarzon dan kwallon kafar duniya, wato Ballon d’Or karo na biyar.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ronaldo ya lashe kyautar karo na biyar jere, inda ya yi kankankan da dan kwallon Barcelona Lionel Messi, ya kuma ce bai yi amannar cewa akwai wani dan wasa da ya fi shi ba.
“Babu dan wasa sama da ni. Ina buga tamaula sosai, ina da sauri, ina da karfi, ina buga kwallo da kai, na ci kwallaye, na taimaka an ci, akwai mutanen da suka fi son Neymar ko Messi, amma na fada babu wanda yake da irin wadannan abubuwan fiye da ni,” in ji dan kwallon.
Ya kara da cewa,” Babu wanda ya lashe kyautuka iri daban-daban kamar ni. Ba ina magana a kan kyautar Ballon d’Or kawai ba ne.”
bbchausa.
Ronaldo ya kuma kara da cewa, tabbas yaji haushi, lokacin da Messi yayita cinye kyautukan Ballon d’or a jere har sau hudu daga shekarun 2009 zuwa 2012.
Kamar yanda ya gayawa Skysports ” Bazan boye ba tabbas naji haushi, na rika bacin rai lokacin da Messi ya rika cinye kyautukan Ballon d’or sau hudu a jere, nine na fara cin kyautar, amma yazo ya wuceni, kai har saida takai ga na kusa hakura saboda na gaji da zuwa gurin gasar amma kullun in rika daukar na biyu”
“Amma ina godewa mutanen da suke tare dani, masu bani shawara, su suka kara karfafamin gwiwa, kuma a yazu babu wani dan wasan kwallo da aka tabayi a Duniya daya kaini”


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Karanta wannan  An saka dokar hana fitar dare a jihar Anambra

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.