fbpx
Thursday, May 26
Shadow

Babar Magana: Naira miliyan 43 sunyi batan dabo a hedikwatar APC yayin da ake sayar da fam din tsayawa takara na zaben 2023

Hedikwatar jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ta fada cikin rudani a ranar Laraba yayin da wasu makudan kudade har Naira miliyan 43 suka bace a harabar ofishin.

Kudaden yan dala ne wanda sun kai dalar Amurka 75,000 kuma ana zargin suna cikin kudaden da jam’iyyar ta tara a ci gaba da siyar da fom din zaben 2023.

Rahotanni sun bayyana cewa, kwatsam an tarwatsa rumfar da ake sayar da fom ba tare da wani bayani ba bayan an gano cewa wadannan kudaden sun bata.

An tattaro cewa kudaden da suka kai dala 75,000 sun bace a daidai lokacin da aka samu cunkoson jama’a a babbar kofar shiga harabar jam’iyyar.

Karanta wannan  Da Dumi Duminsa: Peter Obi ya janye ra'ayinsa na tsawa takarar shugaban kasa kuma ya fice daga jam'iyyar PDP

Sai dai wasu majiyoyin jam’iyyar sun bayyanawa PUNCH cewa kudaden da suka bata ba su da alaka da kudaden sayar da fam din tsayawa takara, domin ana sa ran masu neman tsayawa takara su yi ajiya a lambobin da aka kebe kafin su karbi fom dinsu a gidan Buhari.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.