fbpx
Sunday, February 28
Shadow

Babar Magana: Yan sanda sun kama wani dalibi a jihar Neja saboda rubuta wasikar barazanar satar dalibai a makarantarsa

Rundunar ‘yan sanda reshen jihar Neja ta cafke wani dalibi dan shekara 15, mai Suna, Samaki Azozo, kan zargin tayar da hankulan jama’a.

Kakakin rundunar, DSP Wasiu Abiodun, wanda ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Juma’a 19 ga Fabrairu, ya ce Azozo ya rubuta wata wasika ta barazanar zuwa Kwalejin Kimiyya ta Gwamnati, yana nuna cewa masu satar mutane za su kai hari makarantar.

Dalibin ya rubuta wasikar barazanar ta karya a ranar 16 ga watan Fabrairu 2021, kuma ya likata a kan allon sanarwa na makarantar.

A cikin wasikar an rubuta cewa masu satar mutane za su kai hari makarantar a kowane lokaci, saboda haka, ya kamata ɗalibai da ma’aikatan makarantar su kasance cikin shiri.

A lokacin da ake yi masa tambayoyi, ya amsa cewa ya rubuta wasikar ne don haifar da tashin hankali da rufe makarantar don ba shi damar komawa tsohuwar makarantarsa, Makarantar Sakandaren Gwamnati dake Kuje inda ya halarci karamar Makarantar Sakandare kafin mahaifinsa ya sauya masa zuwa Kwalejin Kimiyya ta Gwamnati.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *