Babban Bankin Najeriya a ranar Litinin ya ce a shirye yake ya saki kimanin masara tan 300,000 a cikin kasuwar kasar a watan Fabrairu.
A cikin wata sanarwa, CBN ya ce za a aiwatar da wannan matakin ne ta hanyar shirinta na Anchor Borrowers kuma ana sa ran zai taimaka wajen rage farashin kayan, da tayar da bukatan ta, da kuma inganta ribar manoma.
Sanarwar da CBN ta shirya ta biyo bayan kokarin da manyan masu ruwa da tsaki da ke aiki tare da gwamnati da hukumomin tsaro suka yi, don kawo karshen kalubalen da masu shiga tsakani, da ‘yan fashi ke haifarwa wujen samun kayan.
Masara a yanzu ana sayar da ita kan N155,000 a kowace metric tonne.