Wani farfesa a babbar jami’ar Oxford dake kasar Ingila, Dr. Tom Crawford ya bayyana cewa Cristiano Ronaldo ne gwarzon dan wasan tamola na duniya.
Babu shakka mutane da dama sun aminta cewa tauraron dan wasan Manchester shine gwarzon dan wasan tamola a tarihi,
Domin ya taka leda a kasashe daban daban a nahiyar turai kuma babu kasar dabe lashe kofuna a cikinta ba.
Sauran ‘yan wasan duniya sun hada da babban abokin hamayyarsa Lionel Messi, Pele, Maradona da dai sauran su.