fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Babbar kotun jihar Ekiti ta yankewa mutumin da yayi lalata da ‘yar shekara 11 hukuncin shekaru hudu a gidan yari

Babbar kotun jihar Ekiti ta yankewa wani mutun dan shekara 59 Dele Adeyanju hukuncin shekaru shekaru uku a gidan yari saboda yayi lalata da wata yarinyar yar shekara 11.

Mai gabatar da kara na kotun, Akinlola Abun ya gabatarwa da mai shari’ai kwararen shaidu hudu, kuma yace ya aikata laifin ne a shekarar 2019.

Inda alkali Bamidele Omotoso ya gamsu da shaidun kuma bai bukaci jin wata shaida daga wurin wanda ake tuhuma ba, sannan ya yanke masa hukuncin shekaru hudu a gidan yari ba beli.

Leave a Reply

Your email address will not be published.