Sojojin Najeriya dake yaki da kungiyar Boko Haram sun kashe ‘yan Kungiyar ISWAP da suka balle daga kungiyar ta Boko Haram su 18.
Sojojin sun kai samame ne maboyar ‘yan Boko Haram din dake Malam Fatori, Gashigar, Talata Ngam, Larki A & B da Kagarwa dake karamar hukumar Abadam dake jihar Borno.
Sojojin sun kuma kwato makamai da kayan Amfanin ‘yan kungiyar da dama.
Sanarwar da hukumar sojojin ta fitar tace zasu ci gaba da farautar ‘yan Kungiyar ta Boko Haram dan ganin an kakkabe sauran mayakanta da suka rage.

