‘Yan Najariya sun koka da yawan tafiye-tafiyen da shugaban kasa, Muhammadu Buhari ke yi zuwa kasashen waje.
Masana masu lura da harkokin siyasa sun ce tunda shugaba Buhari ya hau mulki yake tafiye-tafiye zuwa kasashen waje.
Sun ce amma bai baiwa ziyarar cikin gida muhimmanci musamman ma inda ake bukatarsa.
Sun ce tafiye-tafiyen nasa basa karuwar Najariya da wani abin azo a gani.
Rahoton na Daily Trust yace amma tafiye-tafiyen na shugaban kasar sun samu tsaiko bayan da cutar Coronavirus tazo amma tafa sassautawa sai shugaban ya ci gaba.
A jiya ne dai shugaban kasar ya dawo daga kasar Spain.