Wani babban malamin Kiristanci Archbishop Nwaobia ya bayyana cewa babu alamar lamura zasu gyaru a gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu.
A hirar da wakilin jaridar sunnewsonline suka yi dashi, ya bayyana cewa faduwar darajar Naira akan Dalar Amurka matsala ce babba wadda ta jefa ‘yan Najeriya da yawa cikin halin wahala.
Yace kuma gwamnatin Tinubu ta kasa samo hanyar warware wannan matsala.
Ya kara da cewa, Sam Gwamnatin Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu bata da alkibla dan ta kasa dasa tushen ci gaban Najeriya.