A jiya ne dai hutudole ya kawo muku rahoton yanda surukin shugaban kasa, Ahmad Indimi dake auren diyar shugaban kasar, Zahra Buhari tare da zakinsa da ya siya wanda zai rima kiwo.
Wannan lamari ya dauki hankula sosai musamman a shafukan sada zumunta inda ake ta bayyana mabanbanta ra’ayoyi akai.
Tauraruwar fina-finan Hausa, Rashida Mai Sa’a itaka ta bayyana ra’ayinta kan wannan batu, inda tace babu Amana tsakanin Mutum da Kura, tace Ahmad ya daina dan kuwa suna sonshi ko dan Zahara.
