Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya bayyana cewa babu dan arewar da zai zabi Peter Obi a zabe mai zuwa.
Ya bayyana hakan ne yayin dayake ganawa da manema labarai na Channels inda yace sai yasa basa so su bashi su bashi tikitin shugaban kasa na jam’iyyarsu.
Domin shi ba wai baya so ya janyewa Peter Obi bane amma yana ganin kamar hakan zai sa kowa ya rasa domin jam’iyyar ba zata yi nasara ba.
Saboda yace a halin d kasa ke ciki yanzu ‘yan arewa ba zasu yi dan kudu ba nasu zasu zaba.