Sbugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa babu gadon ya barwa iyalansa musamman yaransa idan ya bar mulki.
Muhammadu Buharin ya bayyana hakan ne yayin da yake shirin barin ofisin shugaban kasa nan da watan Mayu na shekarar 2023.
Inda yace ingataccen Ilimi kadai ya barwa yaran nasa su gada domin shine abu mafi muhimmanci da suka fi bukata.
Shugaban ya bayyana hakan ne kan yajin aikin da ASUU keyi wanda ya cewa abin ya isa hakan su bar yara su dawo makaranta, amma ASUU tace ai shine dalilin daya sa suke yakin aikin.