Babban Malamin addinin Musulunci, Sheik Ahmad Gumi ya bayyana cewa babu laifi a zabar Musulmi da Tinubu yayi a matsayin abokin takararsa.
A ranar lahadi ne Tinubu ya zabi Musulmi dan uwansa, Kashim Shettima a matsayin abokin takararsa na zabe mai zuwa wanda hakan ya jawo cece kuce ganin cewa gabadayansu musulmai ne.
Amma yanzu Sheik Ahmad ya bayyana cewa ba ruwam siyasa da addini kuma Tinubu ya zabi musulmi domin yayi nasarar lashe zabe ba don wani abu na daban ba.