fbpx
Wednesday, March 3
Shadow

Babu maganar Sulhu da ‘yan Bindiga kawai a shiga dajin a kashesu gaba daya, amma wasu gwamnonin sun ki bada hadin kai>>Gwamna El-Rufai

Gwamnan Jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya Nasir Ahmed El-Rufai ya ce rashin haɗin kai tsakanin gwamnonin yankin na daga cikin abubuwan da suka sa aka kasa shawo kan matsalar ‘yan fashi masu garkuwa da mutane.

A hirarsa da BBC, gwamnan ya ce yana da ra’ayin a buɗe wa ‘yan bindigar wuta kuma babu batun sulhu tsakanin gwamnatinsa da masu garkuwa da mutane.

“Idan Gwamnatin Tarayya ba ta ba mu sojoji na sama da na ƙasa ba, an shiga dazukan nan an kashe ‘yan ta’addan nan a lokaci ɗaya, to za mu ci gaba da zama ciikin matsala,” in ji gwamnan.

A cewarsa: “Mu a Kaduna muna haɗa kai da Jihar Neja. Gwamnan jihar na kira lokaci zuwa lokaci muna hada bayanai. Muna abubuwa tare da su.”

Ya bayyana haka ne a yayin da ‘yan bindigar ke ci gaba da cin karensu babu babbaka a yankin.

Kazalika, kalamin nasa ya sha bamban da na wasu gwamnonin yankin wadanda ke ganin yin sulhu da ‘yan bindigar shi ne mafita ga rashin tsaron da ke addabar arewa maso yammacin Najeriya.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *