Reno Omokri ya mayar da martani ga fitaccen limamin Katolika, Fr Oluoma da wasu da dama da suka yi adawa da goyon bayansa kan auren mata fiye da daya.
A cikin wani sakon da aka raba a Instagram, Reno ya ce babu wani nassi da yayi Allah wadai da auren mata fiye da daya.
Ya yi kashedin cewa ya kamata mutane su kasance masu yin amfani da hankalinsu a lokacin da suke karanta Littafi Mai Tsarki (bibul) da kuma fassara shi.