fbpx
Thursday, July 7
Shadow

Babu shari’ar Musulunci a kundin tsari Mulkin Najeriya>>Wanda yayi kalaman Batanci ga Annabi Muhammad (SAW) ya gayawa Kotu

Matashi Yahaya Umar Sharifai da kotun shari’ar Musulunci a Kano ta yankewa hukuncin kisa bisa samunsa da laifin kalaman batanci ga fiyayyen halitta,  Annabi Muhammad (SAW) ya daukaka kara.

 

A cikin takardun daukaka karan da yayi wanda lauyansa, Kola Alapinni ya shigar a gaban babbar kotun Kano, ya bayyana cewa ita kanta jihar Kanon, kundin tsarin mulkin Najeriya ne ya kafata dan haka ba zata iya yin amfani da Shari’ar Musulunci ba.

Yace laifin da yayi baya cikin kundin tsarin mulkin Najeriya dan haka babu Shari’ar Musulunci a cikin kundin tsarin mulkin, ya kuma kara da cewa yana karar gwamna Ganduje saboda kasa samar masa da tsaro da kariya yayin lamarin.

Karanta wannan  Matafiyan babbar Sallah a jihar Kaduna sun koka kan tsadar kudin mota

 

A karshe yayi kira ga kotu ta cire hukuncin kisan da aka masa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.