fbpx
Thursday, May 26
Shadow

Babu shugaban kasa a tarihin Nageriya kamar Buhari – Gwamna Umahi

Gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi, a ranar Alhamis ya yabawa shugaban kasa Muhammadu Buhari, inda ya ce babu shugaban kasa a tarihin Najeriya kamar sa.

Ya jinjinawa Buhari a wajen liyafar karrama shugaban da ya kai ziyarar aiki ta kwanaki biyu a jihar Kudu maso Gabas.

Gwamnan ya yi watsi da ikirarin da ake na cewa Shugaba Buhari ya nuna bangaranci ne yayin da ya ba jihar kudin ayyuka bisa son da yake yi wa jihar.

Gwamnan ya kuma ce; Ta yaya ni a matsayina na Shugaban kasa zan iya mayar wa da gwamnan jam’iyyar adawa Naira biliyan 78 kan aikin da bai yi a shekarar zabe ba? Babu wani Shugaban kasa mai irin wannan halin in ba kai ba. Kai mutumin kirki ne, yallabai kuma muna godiya matuka.

Leave a Reply

Your email address will not be published.