Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya caccaki wanda suke takarar gwamna a tare dashi a karkashin jam’iyyar PDP a jihar ta Borno.
Gwamnan yayi kira ga mabiyansa da su yi watsi da maganar da Muhammad Ali Jajere na PDP yayi a kansa.
Jajere ya zargi gwamna Zulum da bayar da kwangiloli ga abokai da ‘yan uwansa.
Kakakin gwamna Zulum, Isa Gusau ya bayyana Jajere a matsayin wanda babu wanda ya sanshi.
Yace shima da kanshi ya san haka, shiyasa ma yake ta kokarin ganin ya janyo Hankalin kafafen yada labarai dan a sanshi ta hanyar caccakar Zulum.