Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, babu wanda zai takurawa ya ajiye mukaminsa cikin Ministoci da hadimansa kan yana nema wani matsayin siyasa.
Jaridar Punchng ce ta ruwaito wannan labari.
Shugaban ya bayyana cewa, dokar ta hukumar zabe me zaman kanta watau INEC na cike da sarkakiya dan kuwa har ma kotu ta dakatar da ita.
Rahoton yace shugaba Buhari yayi imanin duk wanda ke son ya ajiye mukaminsa cikin masu neman takarar, to yana iya ajiyewa bisa radin kansa amma babu wanda zai takurawa.
Akwai dai mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo, Rotimi Amaechi, da Chris Ngige da suka fito takarar shugabancin Najeriya.
Kuma suna shan matsin lamba akan sai sun ajiye mukamansu kamar yanda dokar INEC ta tanada.