Gwamnan jihar Kogi,Yahaya Bello ya bayyana cewa akwai gwamnonin PDP 10 da zasu koma APC nan ba da jimawa ba.
Gwamnan ya bayyana hakane a hirar da yayi da gidan Talabijin na Channelstv inda yace jam’iyyar su bata cikin rikici.
Yace abinda aka gani a makwannin da suka gabata, wata ‘yar matsala ce ta faru tsakanin ‘yan uwan juna dake jam’iyyar kuma saka bakin shugaban kasa,Muhammadu Buhari ya warware matsalar.
Yace nan gaba kadan gwamnonin PDP 10 zasu koma APC din kuma a jira za’a ga tabbatar wannan bayanin nashi.