Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party, Peter ya bayyana cewa shi bai tsaya takarar shugaban kasa dan taimakawa Atiku Abubakar yayi nasara ba shima nasarar yake nema.
Obi ya bayyana hakan ne yayin dayake ganawa da manema na Channels ranar litinin, inda kuma yace babu wani siddabarun da dan takarar shugaban kasar na PDP zai yi ya doke shi a zaben shekarar 2023.
Peter Obi ya kasance abokin takarar Atiku Abubakar a shekarar 2019 amma duk da haka sun kasa doke shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Wanda hakan yasa yanzu shima Obi ya koma Labour Party ya tsaya takarar shugaban kasa da kansa kuma yace yana ji a ransa cewa shine zai yi nasara.