fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Babu wata gaba tsakanin Kashim Shettima da Malam Nasriu Ahmad El Rufa’i, cewar Uba Sani

Dan takarar gwamnan jihar Kaduna a jam’iyyar APC, Sanata Uba Sani ya bayyana cewa babu wata gaba tsakanin El Rufa’i da Shettima.

Rahotanni da dama sun bayyana cewa El Rufa’i ya fusata sosai bayan Tinubu ya zabi Kashim Shettima a matsayin abokin takararsa domin yasha shi zai zaba.

Wanda hakan yasa wasu ke tunanin cewa gwamnan jihar Kadunan na takun saka da Kashim Shettima amma yanzu Uba Sani ya karyata hakan.

Inda yace wannan rahotannin duk karya ne domin El Rufa’i ne mutun na farko daya fara kiran Shettima ya taya shi murna bayan Tinubu ya zabe shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published.