fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Babu wata gadar da muka gida akan Biliyan 2.3>>NDDC ta karyata hoton gadar katako dake yawo a shafukan sada zumunta

Hukumar kula da ci gaban yankin Naija Delta, NDDC ta karyata hoton gadar Katako dake yawo a shafukan sada zumunta da ake cewa ta gina akan Naira Biliyan 2.3.

 

Hukumar tace wannan labarin ba gaskiya bane. Gadar dake Elebele, Jihar Bayelsa ta rika yawo a shafukan sada zumunta inda akace NDDC ce ta ginata akan Biliyan 2.3.

Saidai a ta bakin daya daga cikin daraktocin NDDC, Charles Obi Odili ya bayyana cewa mutanen yankin sun samesu inda suka bukaci da a gyara musu gadar su da ta rushe. Yace basu kai ga yin aikin ba tukuna.

Karanta wannan  APC ta shigar da karan Tinubu a kotu cewa ta hana shi tsayawa takarar shugaban kasa

 

Yace mutanen yankinne suka yi aikin gayya suka yi wannan gadar katako da ake gani amma ba NDDC ba.

 

Yayi zargin cewa, wasu ne dake son baya sunan ma’aikatar suka dauki nauyin wannan aiki. Inda yace kada mutanen yankin su biye musu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.