fbpx
Tuesday, May 24
Shadow

“Babu yadda za’ayi ina shugaban al’umma ace yarona na makaranta daban da inda yaran talakawa suke: ko ina gwamna ko na sauka: Idan yarona ya cika shekaru 6 zan sakashi makarantar gwamnati”>>Gwamna El-Rufai na Kaduna

Gwamnan jihar Kaduna, malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya kara tabbatar da maganar cewa zai saka danagi makarantar gwamnati idan ya cika shekaru shida da haihuwa, gwamnan ya taba fadin maganar a kwanakin baya. A wannan karin yace yaron nashi shekarunshi 4 kuma yanzu haka Islamiya yke zuwa amma nan da shekaru 6, koda yana matsayin gwamnan jihar Kaduna ko kuma ya sauka, tabbas zai saka dan nashi a makarantar gwamnati.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Gadai sakon da gwamnan ya fitar a dandalinshi na sada zumunta da muhawara:
Dana Abubakar Sadiq yanzu shekaransa hudu, kuma islamiyya ya ke zuwa. In ya cika shekara shida zan sashi a makarantan Gwamnati domin babu yadda za’ayi ina shugabantan Al’umma, kuma ace wai yarona na wani makaranta daban da inda yaran talakawa suke. 
Lokacin muna yara, ya’yan Ministan ilimi na Arewa, Alhaji Isa Kaita, ajinmu daya dasu a nan LEA Kawo. Amma yanzu masu kudi sun kwashe yaran su sun kai su makarantun kudi sun bar yaran talakawa a na gwamnati domin makarantun su cigaba da lalacewa. To mu baza muyi hakan ba da yardan Allah. 
Wasu na ganin wannan magana, wato na saka dana aa makarantar gwamnati, magana ce kawai ta siyasa. Amma Ina alkawarin chewa zan sa shi a makarantar gwamnati ko da kuwa ba ni a matsayin gwamna. Ina kara tabbatar wa al’umma Indai har wannan aikin da muke yi na dawo da martabar ilimi a makarantun gwamnati ya tabbata, mutane da dama suma zasu chire yaransu daga makarantar kudi su dawo na gwamnati. 
Jama’a dai su ci gaba da mana addu’a, Allah ya ba mu ikon sauke nauyin da ke kanmu. 


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Karanta wannan  Wani matashi mai samar da waraka daga cutar makanta ya bayyana a fakistan

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.