Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa, bacin ran ‘yan Najariya ta guda shiyasa bata cire tallafin man fetur ba.
Hakan na kunshene a cikin maganar da kakakin shugaban kasa, Malam Garba Shehu yayi a ganawar da aka yi dashi a gidan talabijin na channels TV, kamar yanda the Cable ta ruwaito.
Yace gwamnati na duba maslahar jama’a a duk sanda zata gudanar da wani tsari dan daukar matsayin da ya dace.
A zamanin tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan dai ya gamu da fushin ‘yan Najariya a lokacin da yayi yunkurin cire tallafin na man fetur.
Wanda daga baya dole tasa ya hakura da wannan aniya tasa.