Kungiyar Malaman Jami’a ta ASUU reshen babban birnin tarayya Abuja ta ce ba zasu janye yajin aiki ba sai gwamnati ta biya musu bukatunsu.
Kungiyar tace sai gwamnati ta cika alkawarin shekarar 2009 data dauka tare da aiwatar dashi kamin su janye yajin aiki.
Wakilin kungiyar, Dr Salawu Lawal ne ya bayyana haka a ganawa da manema labarai.
Yace a shirye yake su koma bakin aiki muddin gwamnati ta aiwatar da abinda suke so.