fbpx
Thursday, June 8
Shadow

Bafa zamu lamucin kwararar Almajirai daga Arewa zuwa Yankinmu ba>>Kungiyar kare muradun Yarbawa

Itama dai kungiyar kare muradun yarbawa ta YWC ta bi sahun takwararta ta kare muradun Inyamurai inda tace bafa zata lamunci kwararar Almajirai daga Arewa zuwa jihohin Yarbawa ba.

 

Shugaban kungiyar, Farfesa Banji Akintoye ne ya bayyana haka a hirar da yayi da Vanguard inda yace jihohin Arewa sun farka inda suke kokarin kashe al’adar Almajiranci data samo Asali a Arewa.

 

Ya kara da cewa gwamnonin jihohin na Arewa na kokarin ganin sun mayar da Almajiran zuwa jihohinsu na Asali, amma Almajiran basa son komawa jihohin nasu.

 

Yace dan hakane suke neman kwarara zuwa jihohin Yarbawa, yace to ba zasu lamunci wannan ba. Yace Almajiran na dauke da cutar Coronavirus/COVID-19,  duk da ba dukansu ba amma wasu daga cikinsu na dauke da cutar Coronavirus/COVID-19, injishi.

Karanta wannan  Lionel Messi zai koma Inter Miami, An yanke shawarar kuma za'a sanar da komawar l shi a cikin sa'o'i masu zuwa

 

Ya kara da yabawa Gwamnonin yankin da suke hana Almajiran shiga jihohinsu inda yace su kara kaimi wajan kulle iyakokin jihohinsu dan Coronavirus/COVID-19 a Arewa ta yi muni.

 

Ya kara da cewa wannan fa ba batun siyasa bane, maganace ta mutuwa da Rayuwa dan haka sam ba zasu lamunta ba.

 

Ya kuma yabawa gwamnonin bisa matakan da suka dauka na yaki da cutar,musamman Gwamnan Legas inda yace abin a yabane.

 

A baya dai kungiyar Inyamurai itama ta baiwa Almajiran dake yankinsu kwanaki 14 su bar yankin ko su ga rashin mutunci.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *