Friday, May 29
Shadow

Bafa zamu rufe kasar mu ba saboda Coronavirus/COVID-19, Allah zai karemu>>Shugaban kasar Tanzania

Shugaban kasar Tanzania, John Magufuli ya kara nanata aniyarsa ta cewa shifa ba zai rufe kasarsa ba saboda cutar Coronavirus.

 

Shugaban ya bayyana hakane a lokacin da ya halarci coci yayin Ibada.

Yace su sun mika lamarinsu ga Allah shine zai karesu, kuma sunanan suna jiran kasashe makwabtansu, idan sun kammala kullen su shigo kasarsu su basu abinci. Yace ba zasu nuna musu banbanci ba.

 

Ana zargin kasar ta Tanzania da kin bayyanawa Duniya yanda lamarin cutar Coronavirus/COVID-19 ke tafiya a cikin kasar inda rabon da aji sun bayar da alkaluman cutar tun Ranar 29 ga watan Afrilu inda sukace suna da mutane 480 da suka kamu da cutar.

 

Saidai hukumar Lafiya ta Duniya, WHO ta bayyana cewa Tanzania na da mutane 509 da suka kamu da cutar inda ta kashe mutane 21, Guda 183 kuma suka warke.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *